in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yar takarar shugabancin Nijeriya ta ce jinyewarta daga takarar ba shiri ba ne
2019-02-05 16:25:42 cri
Tsohuwar 'yar takarar shugabancin Nijeriya karkashin Jam'iyyar ACPN, Oby Ezekwesili, ta musanta zargin da ake cewa ta janye daga tsayawa takarar ne saboda neman mukamin minister.

Oby Ezekwesili, tsohuwar ministar ilimi ta kasar, ta musanta zargin ne yayin wani taron manema labarai da ya gudana jiya a Abuja babban birnin kasar, inda ta ce ta tsaya takarar ne domin kishin kasar da dukkanin al'umma.

Tsohuwar 'yar takarar ta kuma musanta zargin dake cewa ta wawure gudunmuwar da aka bayar na yakin neman zaben shugaban kasa, ta na mai bayyana shi a matsayin siyasa mara nagarta.

Janyewar Oby Ezekwesili wadda ta rike mukamin minista a kasar har sau biyu, kana tsohuwar mataimakiyar shugaban sashen kula da Afrika na Bankin Duniya, ya sa Shugaban kasar mai ci Muahmmadu Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar, su biyu su zama manyan 'yan takara a zaben da za a yi ranar 16 ga watan nan na Fabreru. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China