Lai Mohammed wanda ke wannan tsokaci yayin wani taron manema labarai a Abuja, fadar mulkin kasar a jiya Litinin, ya ce wasu daga bangaren 'yan adawa a kasar na daukar zaben a matsayin ko a mutu ko ai rai wanda hakan bai dace ba.
Jami'in ya kara da cewa, wasu bayanan sirri sun tabbatar da cewa, akwai wani bangare na 'yan adawar dake son daukar matakan gurgunta zaben dake tafe, ciki hadda shirin wasu, na aikewa da tawagogin mutane goma-goma zuwa wasu manyan kasashen duniya, da nufin yada karairayi game da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.
Za dai a gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majalisun dokokin tarayyar Najeriya ne a ranar 16 ga watan nan na Fabarairu, kana a gudanar da na gwamnoni da 'yan majalisun jihohi a ranar 2 ga watan Maris. (Saminu Hassan)