Maharan dai sun yi dirar mikiya ne kan wasu kauyuka 7 dake gundumar Mada a shiyyar Gusau, babban birnin jahar, da yammacin ranar Litinin, inda suka kashe a kalla mutane 15.
Sai kuma kauyen Batauna shi ma a jahar, inda hukomin 'yan sandan suka ce maharan barayin shanu sun hallaka mutanen kauyen kimanin 11 kana suka cinnawa garin wuta da dare.
Jamia'n tsaro sun gano gawar wata mata daga cikin wadanda aka hallaka a gundumar Mada, sannan sun yi awon gaba da mutum guda da wasu mata 6 inda suka yi garkuwa dasu. (Ahmad Fagam)