Jagoran tawagar ayyukan gaggawa, na WHO a Najeriyar Clement Peter ne ya bayyana hakan a jiya Litinin, yayin taron karawa juna sani da aka gudanar albarkacin ranar cutar Cancer ta kasa da kasa ta bana, wadda ke gudana duk shekara a ranar 4 ga watan Fabarairu.
Taken bikin na bana dai shi ne "Ni ne kuma zai yi nasara."
A Najeriya da ma wasu kasashen Afirka da dama, masana sun fi alakanta dalilan kamuwa da cutar da shan taba, da giya, da rashin motsa jiki, da gurbatar yanayi, da kuma cin abinci maras dacewa da gina jiki. (Saminu Hassan)