Ren Limin, shugaban kungiyar Sinawa mazauna Faransa, ya ce yana alfahari da ci gaba cikin sauri da kasar Sin ta samu karkashin jagorancin JKS.
Ya ce kasar ta samu gagarumin nasarori wajen aiwatar da gyare-gyare cikin gomman shekarun da suka gabata, inda ta kara arziki da karfi.
Shi kuwa Liu Kai, mataimakin shugaban kungiyar yayata hadin kan Sinawa a Birtaniya, ya ce ba sakon gaisuwa kadai jawabin shugaba Xi ya kai ga Sinawa mazauna Birtaniya ba, domin ya kara karfafa yakininsu na samun kyakkyawar makoma.
Liu wanda kuma shi ne shugaban gidauniyar YanFu, yakinin nasu ya samo asali ne daga tabbacin da suke da shi cewa, muddin jama'a suka dogara da juna, to babu kalubalen da ba za su iya shawo kansa ba, kana babu wani buri da ba za su cimma ba. (Fa'iza Mustapha)