in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: An bukaci Amurka da ta soke sammacen Cathy Meng
2019-01-29 19:26:18 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya furta a yau Talata cewa, kasar Sin na fatan kasar Amurka za ta soke batun aikewa Canada sammacen mika Madam Cathy Meng, babbar jami'ar kamfanin Huawei na kasar Sin zuwa kasar Amurka.

Geng Shuang ya kara da cewa, kasar Amurka tana ta kokarin shafa wa wasu kamfanonin kasar Sin kashin kaza, da niyyar gurgunta harkokinsu a kasashe daban daban. Hakan, a cewar jami'in na kasar Sin, wata makarkashiyar da aka kulla ce tare da wani buri na siyasa. Saboda haka, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta daina cin zarafin kamfanonin kasar Sin, gami da nuna adalci gare su. Sa'an nan a nata bangare, kasar Sin za ta yi iya kokarin kare hakkin kamfanoninta. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China