Sin: Goyon bayan shirin gudanar da shawarwari kan batun ciniki ta amfani da na'urorin sadarwa wata kyakkyawar alama ce
Dangane da yadda wasu mambobin kungiyar ciniki ta duniya (WTO) 76, ciki har da kasar Sin, suka tabbatar da amincewa da kaddamar da shawarwari kan batun ciniki ta amfani da na'urorin sadarwa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin mista Geng Shuang, ya furta a yau Litinin cewa, lamarin wata alama ce mai nuni ga irin goyon bayan da mafi yawan mambobin kungiyar WTO ke yi ga manufar kasancewar bangarori masu fada a ji da dama a duniya.
Geng Shuang ya ce mambobin kungiyar suna kuma kokarin kiyaye tsarin ciniki mai alaka da wannan manufa, wanda ya dogaro kan ka'idojin kasa da kasa, gami da gudanarwa a karkashin laimar kungiyar WTO.
Wadannan kasashen, a cewar mista Geng, suna fatan ganin tsarin cinikin da ya shafi bangarori daban daban, ya ci gaba da taka muhimmiyar rawa, a kokarin tabbatar da karuwar ciniki a duniya, da ciyar da tattalin arzikin duniya gaba. (Bello Wang)