Sashen kula da kamfanoni na bankin jama'ar kasar Sin ya sanar a yau Litinin cewa, an karbi bayanan da kamfanin S&P Global Inc, mai kula da aikin awon bashi na kasar Amurka ya gabatar, game da aikinsa na bude reshe a birnin Beijing na kasar Sin. Hakan kuma na nufin kamfanin ya samu izinin gudanar da aikinsa a kasuwannin kasar Sin.
Bisa sanarwar da bankin jama'ar kasar Sin, wato babban bankin kasar ya bayar, an ce kasar Sin za ta kara bude kofarta a fannin harkar awon bashi, wato dai za a baiwa karin kamfanonin ketare masu kwarewar gudanar da wannan aiki damar shigowa kasar Sin. (Bello Wang)