Karkashin shirin, za a yi kokarin kyautata fasahar samar da na'urorin da ake bukata, da fara gwada amfani da sabon tsarin sadarwar 5G, inda za a samar da tsarin sadarwa mai inganci a birnin Beijing, wanda zai zama kan gaba a kasar Sin a wannan fanni.
Ana kyautata zaton cewa, zuwa shekarar 2022, cibiyoyin nazarin kimiyya da fasaha da kamfanonin sadarwa dake birnin Beijing, za su mallaki fiye da kashi 5% na daukacin fasahohi masu alaka da 5G, ta haka za a samar da ribar da yawanta zai kai Yuan biliyan 200 (kwatankwacin dalar Amurka biliyan 29.5), sa'an nan za a kafa sabbin kamfanonin da masana'antu masu alaka da wannan fannin, wadanda darajarsu za ta zarce Yuan biliyan 1000 (kwatankwacin dalar Amurka 147.4). (Bello Wang)