Rahoton ya nuna cewa adadin karfin hada hadar cinikin kasar Sin ya karu zuwa kashi 7.5 bisa 100 wanda ya kai dalar Amurka trillion 5.636 a shekarar 2019, yayin da na kasar Amurka ya karu da kashi 3.3 bisa 100 wanda yakai dala trillion 5.529.
A cewar rahoton, an samu bunkasuwar ne sakamakon cigaban da kasar Sin ta samu a fannin bunkasa harkokin saye da sayarwa ta hanyoyin fasahohin zamani. (Ahmad Fagam)