in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNODC ta damu game da karuwar safarar miyagun kwayoyi a yammaci da tsakiyar Afirka
2018-12-20 11:06:24 cri
Babban daraktan hukumar MDD mai yaki da yaduwar miyagun kwayoyi da manyan laifuffuka ko UNODC Yuri Fedotov, ya bayyana damuwa game da karuwar safarar miyagun kwayoyi a yankunan yammaci da tsakiyar nahiyar Afirka.

Yuri Fedotov ya ce wannan lamari na barazana ga kyautatuwar harkokin gwamnati, da tsaro, da ci gaban tattalin arziki, da zamantakewa, da kuma ingancin kiwon lafiyar al'ummun yankunan.

Jami'in wanda ya bayyana hakan, yayin zaman kwamitin tsaron MDDr na jiya Laraba ta kafar bidiyo daga birnin Vienna ya kara da cewa, gungun masu aikata wannan laifi sun kara fadada hada hadar su, ta shigar da hodar ibilis da heroin ta yankunan Afirka zuwa Turai da sauran yankunan duniya.

Don haka a cewar sa, rahoton UNODC na bana, ya nuna yadda yankunan yammaci da tsakiyar Afirka, da ma sassan arewacin Afirka, ke daukar kaso 87 bisa dari na yawan Sinadarai sa maye da aka kwace a duniya baki daya. Kaza lika a cewar jami'in, yankunan sun samu karuwar masu amfani da kwayar tramadol, wadda ake sha domin maye.

Mr. Fedotov ya ce wannan kalubale na zuwa ne a gabar da yankunan ke fama da matsalolin tsaro daban daban, ciki hadda fataucin makamai da mutane, da safarar haramtattun kudade, da laifuka da ake aikatawa ta yanar gizo, da fashin teku, da barazanar 'yan ta'adda da makamantan su.

Daga nan sai ya bayyana burin UNODC, na ci gaba da tallafawa yankunan biyu, da hadin gwiwar sauran kungiyoyin shiyya shiyya da na kasa da kasa, wajen shawo kan wadannan tarin matsaloli. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China