in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya mika sakon ta'aziyya ga ministan harkokin wajen Kenya kan harin ta'addanci
2019-01-20 16:25:31 cri

Kwanan baya, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya mika sakon ta'aziyya ga takwararsa ta kasar Kenya Monica Juma, bisa harin ta'addancin da ya abku a Nairobi, hedkwatar mulkin kasar.

A cikin sakon, Wang Yi ya bayyana cewa, ya yi matukar bakin ciki da mamaki da jin labarin afkuwar harin ta'addanci a birnin Nairobi, wanda ya haddasa mutuwar mutane masu yawa da jikkata wasu da dama. Ya ce yana mika ta'aziyya ga wadanda harin ya rutsa da su, kana yana jajantawa wadanda suka jikkata da iyalan wadanda suka mutu.

Ban da wannan Wang Yi ya ce, kasar Sin ta yi tir da duk wani lamarin ta'addanci na nuna karfin tuwo, za ta ci gaba da marawa Kenya baya wajen yaki da ta'addanci, da kiyaye tsaro da kwanciyar hankali a kasar.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China