in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nan da kwanaki 100 za'a fara bikin fasahohin aikin lambu na duniya na birnin Beijing
2019-01-19 17:15:34 cri
Daga ranar 19 ga wata, saura kwanaki 100 za'a bude bikin baje kolin fasahohin aikin lambu na duniya na birnin Beijing na shekarar 2019. An ce, an shirya bikin ne a fannoni daban daban yadda ya kamata, ana sa ran, yawan mutanen da zasu halarci bikin zai kai kimanin miliyan 16, kuma yawan kasashen da kungiyoyin duniya da zasu halarci bikin mai yiwuwa zai kai matsayin farko bisa na bukukuwan irin na matsayin A1 da aka gudanar a baya.

Bikin fasahohin aikin lambu na duniya biki ne da kungiyar masu aikin lambu ta duniya ta amince a gudanar dashi. Domin bikin zai kawo babban tasiri da moriya ga wurin da aka gudanar dashi, birane da dama na duniya suna kokarin neman samun bakuncin gudanar dashi. Za a gudanar da bikin na bana a unguwar Yanqing dake birnin Beijing na kasar Sin a ranar 29 ga watan Afrilu.

Ya zuwa yanzu, kasashe 86 da kungiyoyin duniya 24 sun tabbatar da zasu halarci bikin a wannan karo, yawansu zai kai matsayin farko bisa na dukkan bakukuwan fasahohin aikin lambu a duniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China