in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Venezuela ta katse huldar jakadanci da Amurka
2019-01-24 10:14:22 cri
Jiya Laraba, shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro Moros ya sanar da katse huldar jakadanci dake tsakanin kasarsa da kasar Amurka.

Yayin taron gangami da aka yi a wani wuri dake kusa da fadar shugaban kasar a jiyan, shugaba Moros ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta yanke shawarar katse huldar jakadanci da ta siyasa da kasar Amurka sabo da yadda kasar Amurka ke ta hura wutar neman sauya mulki a cikin kasar Venezuela.

Kafin haka shugaban ya sa hannu kan wata takarda, inda ya bukaci dukkanin ma'aikatan diflomasiyyar ofishin jakadancin kasar Amurka dake kasar Venezuela da su fice daga kasar cikin awo'i 72. Haka kuma, ya ce, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya goyi bayan mamban jam'iyyar adawa, kana shugaban majalisar dokokin kasar Juan Guaido, don ya zama mukaddashin shugaban kasar. Matakin, a cewar shugaba Moros, ya zama tamkar rashin hankali ne.

A jiya ne dai, Juan Guaido ya ayyana kansa a matsayin mukaddashin shugaban kasar Venezuela a wani taron magoyon bayan jam'iyyar adawa da aka shirya. Daga bisani ne kuma, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fitar da wata sanarwa, inda ya amince da Juan Guaido a matsayin mukaddashin shugaban kasar Venezuela. Haka kuma, ya ce, gwamnatin kasar Amurka za ta ci gaba da matsa wa gwamnatin kasar Venezuela lamba ta fannonin tattalin arziki da diflomasiyya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China