Wata sanarwa da sakataren baitulmalin Amurka Steven Mnuchin ya raba wa manema labarai ta bayyana cewa, takunkumin da Amurka ta kakabawa shugaba Maduro ya bayyana adawar da Amurka ke nuna wa kararawa kan manufofin gwamnatinsa.
A don haka sanarwa ta yi gargadin cewa, duk wanda ya goyi bayan kafa majalisar dokokin, zai iya fuskantar takunkumi daga gwamnatin Amurka a nan gaba.
Takunkumin dai ya shafi kwace dukkan kadarorin Nicolas Maduro, an kuma haramtawa Amurkawa yin mu'amula da shi.
Sai dai kuma, shugaba Maduro ya fito a jiya Litinin, yana watsi da takunkumin na kasar Amurka, ya ce, yana alfahari, ganin yadda Amurka ke hakonsa. (Ibrahim)