in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An jefa kuri'ar yiwa kundin tsarin mulki gyaran fuska a kasar Venezuela
2017-07-31 12:47:42 cri
Tun da misalin karfe shida na safiyar jiya Lahadi agogon wurin ne, aka fara jefa kuri'a na yiwa kundin tsarin mulki gyaran fuska a Venezuela. A halin yanzu ana gudanar da aikin jefa kuri'ar lami-lafiya.

Shugabar hukumar zaben kasar Venezuela Madam Tibisay Lucena ta bayyana cewa, kawo yanzu ba'a samu rahoton barkewar tashin hankali ko wasu dake kokarin kawo cikas ga wannan shiri a kasar ba.

A jiya ne shi ma shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya jefa tasa kuri'ar a wata mazaba dake birnin Caracas, inda ya yi kira ga daukacin al'ummar kasar da su fito kwansu da kwarkwatarsu don jefa tasu kuri'ar, yana mai jaddada cewa, babu wani mutumin da zai kawo tsaiko ga al'ummar Venezuela don su jefa kuri'a.

Maduro ya ce, yana fatan kasashen duniya za su mutunta gami da nuna goyon-baya ga jama'ar Venezuela don su bayyana ra'ayinsu na demokuradiyya ta hanyar jefa kuri'a.

Al'ummar Venezuela sama da miliyan 19 ne za su zabi membobi 537 daga cikin dukkan mambobi 545 wadanda za su yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska. Za a zabi sauran 8, 'yan yanki na asali a ran 1 ga watan Agusta. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China