in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Maduro na Venezuela ya tsallake riga da baya
2018-08-05 15:49:43 cri
Ministan sadarwa na kasar Venezuela Jorge Rodriguez ya tabbatar a jiya Asabar cewa, shugaba Nicolas Maduro na nan kalau, biyo bayan wani hari da aka kai masa.

Harin da aka kaiwa shugaban da wasu jirage marasa matuka dauke da abubuwan fashewa ya faru ne a dai-dai lokacin da shugaba Maduro ke yiwa sojoji sama da 17,000 jawabi a bikin cika shekaru 81 da kafa sojojin tsaron kasar. Bayanai na cewa, shugaban na nan kalau sai dai sojoji 7 sun jikkata.

Sai dai a wani jawabin da ya gabatar daga bisani ta kafofin talabijin na kasar, shugaban ya dora alhakin hari kan kungiyoyin 'yan adawa masu tsattsauran ra'ayi dake Venezuela da kasar Colombia tare da hadin bakin kasar Amurka.

Shugaban ya kuma kira harin a matsayin yunkuri na halaka shi.(Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China