in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bolton ya musanta zargin da aka yiwa Amurka na yunkurin hallaka Maduro
2018-08-06 11:49:55 cri

Babban mashawarci kan harkar tsaro na gwamnatin Amurka John Bolton ya fada a jiya Lahadi cewa, gwamnatin Amurkar ba ta da hannu a yunkurin baya bayan nan na hallaka shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro.

Bolton ya shedawa jaridar "Fox News Sunday" cewa, "Zan iya cewa na yi amana gwamnatin Amurka ba ta da hannu ko kadan a wannan yunkurin."

Bolton ya fadi hakan ne ga jami'in dake kula da harkokin diplomasiyya kasar Amurka a Caracas kana ya bayyana cewa Amurkar tana da dalilan kare kanta daga wannan zargi.

Shugaba Maduro ya tsallake rijiya da baya daga wani yunkurin harin da aka kai masa ta jirgin sama marar matuki a daren ranar Asabar, a daidai lokacin da mista Maduro ke gabatar da jawabin cika shekaru 81 da kafuwar rundunar tsaron kasar.

Daga bisani, Maduro ya bayyana harin da cewa wani yunkuri ne na neman hallaka shi, kana ya dora alhakin harin kan wasu dake adawa da gwamnatinsa a Venezuela, da Colombia da kuma makarkashiya daga gwamnatin Amurka.

A martanin da ya mayar, Bolton ya ce "idan har gwamnatin Venezuela tana da wasu bayanai da take son gabatar mana wadanda ke nuna yiwuwar Amurka ta aikata wani laifi na saba doka, za mu duba lamarin mai tsanani."

Tun bayan da aka sake zabar Maduro a shugaban kasar, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya amince da wata dokar ofishin shugaban kasa inda ya haramtawa duk wani mutum ko wata hukumar daga Amurka yin hada hadar ciniki da gwamnatin Venezuela.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China