in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a zuba jari bisa bukatun al'umma yadda ya kamata, in ji kwamitin yin kwaskwarima da raya kasar Sin
2019-01-15 13:30:31 cri
Yau Talata, mataimakin shugaban kwamitin yin kwaskwarima da raya kasar Sin Lian Weiliang ya bayyana cewa, a shekarar bana, za a ci gaba da karfafa ayyukan zuba jari a kasar Sin, da kuma mai da hankali kan zuba jari bisa bukatun al'umma.

Ya ce, a bana, za a karfafa ayyukan gina ababen more rayuwa a sabbin fannoni, wadanda suka hada da fasahar kwaikwayar tunanin bil Adama, da yanar gizo ta masana'antu, da kuma fasahar intanet ta 5G mai amfanawa harkokin kasuwanci. A sa'i daya kuma, za a karfafa ayyukan gina ababen more rayuwa a birane da karkara, da ayyukan sufurin kayayyaki, da kawar da talauci, da kuma raya makamashi da dai sauransu. Bugu da kari, ya ce, za a ba da karin tallafi ga al'umma, musamman ma a fannonin ba da ilmi, da kiwon lafiya, da kuma kiyaye tsofaffi da sauransu.

Kana, za a dukufa wajen kare muhalli, da karfafa ayyukan yin rigakafi kan bala'u. Haka kuma, za a inganta fasahohin kirkire-kirkire, yayin da kuma ake sabunta na'urorin da ake amfani da su. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China