in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron dandalin daga matsayin tattalin arzikin Sin gaba karo na 10 a Beijing
2019-01-12 20:26:21 cri
Yau Lahadi, an shirya taron dandalin tattauna matakan daga matsayin tattalin arzikin Sin gaba karo na 10 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Kuma babban taken taron shekarar bana shi ne "Sabbin damammakin raya masana'antu a sabon lokacin aiwatar da gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje".

A yayin taron, shugaban cibiyar nazarin ci gaban kasa na majalisar gudanarwar Sin Li Wei, ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana fuskantar sauye-sauyen yanayin tattalin arziki a kasar Sin, har ma da kasashen duniya baki daya. Kuma tattalin arzikin kasar Sin yana ci gaba da bunkasuwa cikin yanayi mai kyau, a halin yanzu, da kuma cikin dogon lokaci mai zuwa, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da kasancewa cikin muhimmin yanayi na neman bunkasuwa bisa manyan tsare-tsare. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China