in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin kasar Sin ya bukaci sake duba na tsanaki game da takunkumin MDD kan Sudan
2019-01-18 10:44:00 cri
Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya bukaci kwamitin tsaron MDD, da ya nazarci takunkumin da aka kakabawa kasar Sudan, duba da kyautatuwar yanayin tsaro a yankin Darfur.

Wu Haitao, ya ce lokaci ya yi da za a duba wannan takunkumi, a kuma yi gyara daidai da yanayin da ake ciki, ta yadda za a kai ga janye takunkumin baki daya.

Ya ce hakan zai aike da kyakkyawan sako ga kasashe masu ruwa da tsaki a batun kasar ta Sudan, zai kuma tallafawa gwamnatin kasar wajen daukar matakan wanzar da zaman lafiya, da daidaito a yankin na Darfur.

Jami'in na wannan tsokaci ne yayin da kwamitin dake lura da sanya takunkumi MDD, ya gabatarwa kwamitin na tsaro bayani game kasar ta Sudan.

Mr. Wu ya kuma ja hankalin kasashen duniya, da su shiga a dama da su wajen tallafawa gwamnatin kasar Sudan da dabarun kyautata tsaron ta, da na kyautata ayyukan gwamnati, tare da tabbatar da ganin dakarun tsaron kasar sun dauki nauyin wanzar da zaman lafiya ba tare da bata lokaci ba.

Bayanan dai sun nuna cewa, yanayin tsaro a Darfur ya kyautata, kuma gwamnatin Sudan na aiki tukuru wajen sake gina yankin, da kyautata sanin makamar aikin hukumomi, da inganta tsaro a yankin. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China