in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zan dukufa wajen warware matsalar Syria ta hanyar siyasa, in ji sabon manzon musamman na MDD kan batun Syria
2019-01-16 10:53:02 cri
Jiya Talata, sabon manzon musamman na babban magatakardan MDD kan batun Syria Gil Petersen ya bayyana a birnin Damascus, fadar mulkin kasar Syria cewa, zai dukufa wajen warware matsalar Syria ta hanyar siyasa.

A wannan rana, Mr. Petersen ya isa birnin Damascus, inda ya fara ziyarar aiki ta farko a kasar, a matsayin manzon musamman na MDD kan batun Syria.

Haka kuma, Mr. Petersen ya gana da mataimakin firaminista, kana ministan harkokin wajen kasar Syria Walid Al-Moualem, inda suka tattauna yadda za a gaggauta ayyukan warware matsalar Syria ta hanyar siyasa. Ya ce, zai saurari ra'ayoyin gwamnatin kasar Syria, da kuma dukufa wajen warware matsalar bisa kundin tsarin MDD, da kuma kudurorin kwamitin sulhu na MDD.

Kana, ya ce, MDD tana goyon bayan kasar Syria wajen kiyaye mulkin kai, da 'yancin kai, da kuma kasancewar kasar daya tak.

A nasa bangare kuma, Walid Al-Moualem ya taya Mr. Petersen murnar kama aiki a matsayin manzon musamman na babban magatakardan MDD kan batun Syria. Ya ce, kasar Syria tana son yin hadin gwiwa da shi, domin inganta ayyukan warware matsalar kasar ta hanyar siyasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China