Madam Espinosa ta kuma yaba da gudummawar da kasar Sin ta bayar ta fannin tinkarar matsalar sauyin yanayi, inda ta ce, Sin ta yi matukar kokari wajen magance matsalar sauyin yanayi, kana ta cika alkawarinta a wannan fanni.
Har wa yau, yadda kasar Sin ta yi nasara tsame mutane sama miliyan 700 daga kangin talauci ya baiwa madam Espinosa kwarin-gwiwa sosai. Ta ce, hakika wannan gagarumar nasara ce, kuma Sin babbar kasa ce dake taimakawa ga cimma muradun MDD na samun dauwamammen ci gaba nan da shekara ta 2030.(Murtala Zhang)