in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin kasar Sin ya bukaci samar da tallafin kasa da kasa domin tallafawa tsaro a Mali
2019-01-17 10:16:50 cri
Mataimakin wakilin dindindin a kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya yi kira ga kasashen duniya, da su samar da taimakon sanin makamar aiki a fannin tsaro ga kasar Mali, ta yadda kasar za ta iya tunkarar kalubalen yaki da ta'addanci, da sauran matsalolin tsaro a sassan arewaci da tsakiyar kasar.

Wu Haitao, wanda ke tsokaci yayin zaman kwamitin tsaro na jiya Laraba, ya ce zaman lafiya da tsaro a kasar Mali suna da alaka ta kusa, da tsaron dukkanin yankin da kasar take, don haka dole ne a dauki managartan matakan yaki da ta'addanci, da za su shafi kasar da kewayen ta.

Jami'in ya kara da cewa, Sin ta gamsu da irin kwazon da kasar da al'ummarta suke yi, wajen aiwatar da yarjejeniyar shekarar 2015, wadda ta shafi wanzar da zaman lafiya da sulhu, matakin da ya haifar da gagarumar nasara.

To sai dai kuma jami'in na Sin ya ce, yanayin tsaro a arewaci da tsakiyar Mali na kara tabarbarewa, inda ake samun karin ayyukan 'yan ta'adda, don haka a cewarsa, akwai bukatar tallafi daga kasashen duniya, wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro, tare da ci gaban kasar baki daya. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China