Wannan sanarwa ta ce, yawancin alkalan kotun duniya sun yarda da cewa, masu gabatar da kara ba su samar da cikakkun shaidu, na tabbatar da laifukan da ake zargin Laurent Gbagbo da aikatawa ba, ciki hadda haddasa tashin hankalin da ya abku a kasarsa bayan babban zaben da ya gudana a shekarar 2010.
Bayan kammala babban zaben kasar Kodibwa a karshen shekarar 2010, shugaban kasar na lokacin Laurent Gbagbo, da mai jagorantar 'yan adawa Alassane Ouattara, dukkansu sun ayyana kan su a matsayin masu nasara a zaben, kuma sun yi rantsuwar kama aiki bisa radin kansu. Daga bisani, masu goyon bayan mutanen 2 sun yi taho-mu-gama har tsawon watanni 5, lamarin da ya haddasa rasa rayukan mutane kimanin 3000, kana wasu fiye da miliyan 1 suka galabaita.
A ranar 11 ga watan Afrilun shekarar 2011, aka kama Laurent Gbagbo a Kodibwa, sakamakon yadda masu gabatar da kara na kotun duniya, suka zarge shi, da masu goya masa baya, da daukar matakan karfin tuwo kan jama'a masu goyon bayan Alassane Ouattara, zargin da Laurent Gbagbo ya karyata. (Bello Wang)