in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban Afrika ta kudu ya ce sauya tsarin mallakar gonaki zai kawo hadin kan kasa
2018-12-25 09:58:56 cri

Mataimakin shugaban kasar Afrika ta kudu David Mabuza, ya sanar a jiya Litinin cewa, warware takaddama game da batun mallakar filaye a kasar zai ba da gagarumar gudunmowa wajen tabbatar da hadin kai, fahimtar juna da kyautata zamantakewar al'ummar kasar.

Da yake gabatar da sakon gwamnati na bikin kirsimetin wannan shekara ga al'ummar kasar, Mabuza ya nanata muhimmin sauye fasalin tsarin mallakar gonaki a kasar, yana mai cewa, wannann batu ya riga ya shiga zukatan al'ummar kasar tun kaka da kakanni.

"Sauya tsarin mallakar gonaki zai hada kansa," in ji Mabuza, sai dai ya yi watsi da sukar da wasu ke yi na cewa, batun ya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al'ummar kasar Afrika ta kudun.

Domin shawo kan wannan al'amari da sauran kalubaloli, mun yi amanna cewa, hadin kai wani muhimmin ginshiki ne wajen samar da daidaito a tsakanin al'umma wanda shi ne abin da dukkan mu muke da burin ya tabbata, in ji Mabuza.

Hadin kai shi ne abin da muke ta fafutuka a tsawon rayuwarmu domin ceto al'ummar dake tafe a nan gaba, in ji shi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China