in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF: Yankin kudu da hamadar Sahara na bukatar guraben ayyukan yi a kalla miliyan 20 a duk shekara
2018-12-18 09:34:27 cri

Babbar daraktar asusun ba da lamuni na IMF Christine Lagarde, ta ce yankin kudu da hamadar Saharar Afirka, na bukatar guraben ayyukan yi da yawan su ya kai a kalla miliyan 20 a duk shekara. Lagarde ta bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin wani taron karawa juna sani mai taken "Makomar ayyukan yi a yankin kudu da hamadar Sahara".

Yayin taron na yini 3 da ke gudana a kasar Ghana, jami'ar ta ce, mizanin bukatar guraben ayyukan yi zai daga, sakamakon hasashen da ake yi na karuwar yawan al'ummar yankin. Ta ce bisa hasashen masana, yawan al'ummar wannan yanki zai karu daga mutane biliyan 1 a yanzu, zuwa biliyan 1.7 nan da shekarar 2040.

Kaza lika jami'ar ta IMF ta ce, yawan ma'aikata 'yan kwadago a yankin zai karu da kusan rubi daya, sama da na shekaru 10 da suka gabata. Bisa wannan hasashe ne kuma, ta ce yankin ke bukatar karin guraben ayyukan yi miliyan 20 duk shekara.

Lagarde ta ce, idan har aka kai ga cimma burin hakan, nahiyar Afirka za ta amfana a tsawon lokaci, albarkacin karuwar yawan al'ummar ta.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China