in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwarewar Sin za ta taimaka wajen bunkasa masana'antun Afirka
2018-12-19 09:44:26 cri

Kwarewar Sin a fannin kafa yankunan masana'antu a shekaru 40 da suka gabata, za ta taka rawar gani matuka wajen bunkasa masana'antun nahiyar Afirka.

Masani a fannin tattalin arziki, kuma mataimakin cibiyar nazari game da cinikayyar kasa da kasa da raya tattalin arziki ta kasar Sin wato CAITEC Qu Weixi, shi ne ya bayyana hakan, yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, a gefen taron baje kolin kasashen Afirka, irin sa na farko da ya gudana a birnin Alkahiran kasar Masar, tsakanin ranekun 11 zuwa 17 na watan Disambar nan.

Qu Weixi ya ce, kafawa, da aiwatar da manufofin raya yankunan masana'antu, za su ingiza ci gaban bunkasar masana'antun nahiyar Afirka. Ya ce, a shekarar 2015, kungiyar hadin kan Afirka ta AU ta gabatar da ajandar bunkasa nahiyar nan da shekarar 2063, kuma a cikin tsarin bayanan manufofin, sashen inganta kere kere, zai samu habakar da ta kai a kalla rubi 5 sama da abun da nahiyar ke da shi a yanzu.

To sai dai kuma a cewar Qu, a halin da ake ciki yanzu, sashen kere kere na nahiyar Afirka na samar da GDPn da bai wuce kaso 11 bisa dari na daukacin GDPn nahiyar ba, yayin da bunkasar masana'antun nahiyar ke ja da baya. Har wa yau cikin kasashen nahiyar 55, uku kacal ne ke cikin jerin masu saurin bunkasa a fannin ci gaban masana'antu.

Masanin ya kara da cewa, kasashen Afirka 13 na da burin kafa yankunan raya masana'antu, yayin da ake tsarawa ko ci gaba da ginin irin wadannan yankuna har 20 a tarayyar Najeriya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China