in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Afrika ta kudu da Zambia sun bukaci a bayyana sakamakon zaben DRC
2019-01-10 10:36:07 cri

Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa da takwaransa na kasar Zambia Edgar Lungu sun bukaci hukumar zabe mai zaman kanta (CENI), ta jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC, da ta bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar.

Lungu, shugaban kungiyar raya ci gaban kasashen kudancin Afrika (SADC), babban jigo ne a harkokin siyasa, tsaro, da hadin gwiwar tabbatar da zaman lafiya, yana ziyarar aiki ne a kasar ta Afrika ta kudu.

"Shugabannin kasashen Afrika ta kudu da Zambia wato Ramaphosa da Lungu, sun bukaci CENI da ta hanzarta kammala kirga kuri'un, kana ta gaggauta sanar da sakamakon zaben domin tabbatar da sahihancin zaben," in ji kakakin sashen hulda da kasashen waje na kasar Afrika ta kudu Ndivhuwo Mabaya.

"Shugabannin kasashen biyu sun bayyana cewa, ci gaba da yin jinkiri wajen bayyana sakamakon zaben zai iya haifar da zarge zarge da kuma haddasa rashin zaman lafiya a kasar." in ji Mabaya.

"Shugabannin kasashebn biyu sun kuma yi kira ga dukkan jam'iyyun siyasar kasar da dukkan al'ummar kasar ta Kongo da su kwantar da hankalinsu, kana su baiwa hukumar zaben kasar ta CENI hadin kai wajen sauke nauyin dake wuyanta na bayyana sakamakon zaben," a cewar Mabaya.

A ranar 30 ga watan Disambar shekarar da ta gabata ne aka gudanar da zabe a jamhuriyar Kongo, kana an ayyana ranar 6 ga watan Janairu a matsayin ranar da za'a bayyana sakamakon zaben.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China