in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zurfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka yana da muhimmanci ga makomar dangantakar tsakanin kasashen biyu
2019-01-09 15:19:21 cri
Shugabannin bangarorin siyasa da ciniki na kasar Amurka da dama sun bayyana a birnin New York a daren ranar 7 ga wata cewa, a yayin cika shekaru 40 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Amurka da Sin, kasashen biyu suna bukatar juna da ci gaba da hada kai tare a kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya gaba daya.

A yayin liyafar shekarar 2019 da aka shiryawa kungiyar cinikayya ta kasar Sin dake kasar Amurka, tsohon shugaban kamfanin AIG kuma babban jami'in kamfanin Maurice Greenberg ya yi imanin cewa, za a samu kyakkyawar makoma kan dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin.

Mr Greenberg yana daya daga cikin 'yan kasuwa na kasashen waje da suka zuba jari tare da kafa kamfani a kasar Sin a shekaru 70 na karni na 20, wanda ya ga babban canji da kasar Sin ta samu a cikin shekaru 40 da aka bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a kasar Sin. A kwanakin baya ne, aka baiwa Mr Greenberg lambar yabo ta sada zumunta da yin kwaskwarima ta kasar Sin bisa kokarin sa na raya hadin gwiwar tattalin arziki dake tsakanin Amurka da Sin, da kokarin sada zumunta da samun moriyar juna a tsakaninsu.

Mr Greenberg ya bayyana cewa, ko da yake ana fuskantar matsala kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, amma ci gaban dangantakarsu zai warware matsalolin sassan biyu, da kara bunkasa dangantakarsu zuwa gaba.

Tsohon shugaban kasar Amurka Jimmy Carter ya bayyana a cikin wasikar murnar shirya liyafar a wannan rana cewa, yayin da ake fuskantar kalubale kan raya dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin da ba a saba gano a baya ba, akwai bukatar kara yin mu'amalar tattalin arziki da ba da ilmi da al'adu a tsakaninsu, ta yadda za a raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Jakadan Sin dake kasar Amurka Cui Tiankai da wasu jama'a daga bangarorin siyasa da ciniki na kasar Sin kimanin 450 ne suka halarci liyafar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China