Shugaba Trump wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Tweeter, ya ce bangarorin biyu na kokarin ganin kamfanin ya ci gaba da gudanar da harkokinsa yadda ya kamata. Ya ce ya umarci ma'aikatar kasuwancin Amurkar da ta warware wannan matsala.
A tsakiyar watan Afrilun wannan shekara ce dai aka tilastawa kamfanin ZTE daya daga cikin manyan kamfanoni dake kera nau'rorin sadarwa a duniya dakatar da ayyukansu a duniya baki daya, bayan da ma'aikatar kasuwancin Amurka ta haramtawa kamfanonin kasar fitar da kayayyakin kamfanin.
Yanzu haka dai kamfani na ZTE yana tattaunawa da bangaroirin da wannan batu ya shafa don ganin an warware wannan batu, yana mai jaddada cewa, yana dora muhimmanci wajen martaba dokar hana fitar da nau'rorin da aka sanya masa.(Ibrahim)