A ganin Ahern, tattalin arzikin Sin ya samu ci gaba, wanda ya shaida kyakkyawan yanayin sayen kayayyaki a kasar Sin, kana aikin kwaswarima kan tsarin samar da kayayyaki bisa bukatu ya taka muhimmiyar rawa a wannan fanni.
Kana Ahern ya kara da cewa, yadda ake kara kashe kudi a kasar Sin da aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" sun samar da babbar dama ga kamfanonin Sin da na kasashen waje. Haka zalika kuma, farfadowar tattalin arzikin duniya ya kara bukatar kayayyaki da hidimar kasar Sin. (Zainab)