in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Amurka ya rattaba hannu kan wata takardar kara haraji kan kasar Sin duk kuwa da kashedin da aka yi masa
2018-03-23 12:08:03 cri

Duk da kashedin da kungiyoyin 'yan kasuwa da masana harkokin cinikayya suka yi, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wata takarda dake da nufin kara harajin da ya kai dala biliyan 60 kan kayayyakin da kasar Sin ke kaiwa kasar, matakin dake ke barazana ga harkokin cinikayya a duniya.

Shugaba Trump ya umarci wakilin cinikayya na kasar Robert Lighthizer ya wallafa jerin kayayyakin kasar Sin da harajin zai shafa cikin kwanaki 15, yayin da ya ba baitulmalin kasar kwanaki 60 na gabatar da iyaka kan jarin kasar Sin a Amurkar.

Kafin rattaba hannu kan takardar, shugaba Trump ya ce, harajin zai kai dala biliyan 60, sai dai wani babban jami'i a fadar White House ya shaidawa manema labarai cewa, adadin ya kusa kai wa dala biliyan 50.

Umarnin na zuwa ne bayan kasar Sin da kungiyoyin 'yan kasuwar Amurka sun yi kashedi da kakkausar murya game da matakin a makonnin baya-bayan nan.

A wata wasika da suka aikewa Trump a ranar Lahadi da ta gabata, kungiyoyin 'yan kasuwa 45 na Amurka na bangarorin fasaha da sauran kayayyakin amfani, sun bukaci gwamnatin kada ta dauki matakin domin zai yi illa ga masu sayyaya da kamfanonin kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China