in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha na sa ido kan jirgin ruwan soja na Amurka da ya shiga bahar Aswad
2019-01-08 10:17:18 cri
Kafofin watsa labarun kasar Rasha sun ruwaito wata sanarwar ma'aikatar tsaron kasar dake cewa, jirgin ruwan soja na kasar Amurka mai suna Fort McHenry na aiki a yankin bahar Aswad, kuma bangaren Rasha na sa ido a kansa.

Rahotanni na cewa, jirgin ruwan na Fort McHenry ya shiga yankin bahar Aswad ne a ranar 6 ga wata da karfe 9 na yamma bisa agogon Moscow, kuma ya shiga tashar jiragen ruwa na Constanta ta Romania a ranar 7 ga wata da karfe 9 da minti 30 na safe bisa agogon Moscow. Yanzu haka wani jirgin ruwan tsaro na soja na rundunar jiragen ruwan sojan kasar Rasha dake bahar Aswad na daukar matakai don sa ido a kai.

A ranar 25 ga watan Nuwamba na shekarar 2018, rikici tsakanin kasashen Rasha da Ukraine ya barke a tekun bahar Aswad, sai dai ko wane bangare na kokarin kare kansa. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China