in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Senegal ya gana da Wang Yi
2019-01-07 11:05:40 cri
A ranar 6 ga wata a fadar shugaban kasar Senegal dake birnin Dakar, shugaban kasar Senegal Macky Sall ya gana da memban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi.

Shugaba Sall ya taya murnar saukar na'urar binciken duniyar wata ta kasar Sin, ya ce wannan ya shaida cewa, fasahohin Sin a fannin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha sun zama a matsayi na gaba a duniya, kasashen Afirka sun yi farin ciki game da wannan, yana fatan za a kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a wannan fanni. Wang Yi ya bayyana cewa, nasarorin Sin su ne nasarorin kasashe masu tasowa. Kasashe masu tasowa suna da iko da karfi wajen samun ci gaba cikin sauri a fannin kirkire-kirkire. Sin tana son karfafa hadin gwiwa tare da kasashen Afirka a wannan fanni.

Sall ya bayyana cewa, a dogon lokaci, Sin ta girmama 'yancin kai da ikon mallaka da al'adu na Afirka, da tsayawa tsayin daka kan ra'ayin gudanar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, da tabbatar da moriyar kasashe masu tasowa. Sin da Afirka sun nuna girmamawa ga juna da samun moriyar juna da kuma samun ci gaba tare. Kasar Senegal ta yi kokarin zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakaninta da kasar Sin, za ta nuna goyon baya ga kasar Sin a kan harkokin kasa da kasa. Senegal tana son yin kokari tare da kasar Sin wajen sa kaimi ga aiwatar da ayyukan da aka tsara a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka.

Wang Yi ya bayyana cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa ne. Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga raya kasashen Afirka bisa buri da bukatun kasashen Afirka yadda ya kamata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China