A jawabin da ya gabatar yayin taron kwamitin sulhun MDD kan halin da ake ciki a yankunan dake kewaye da tafkin Chadi, Wu ya bayyana cewar, aikin yaki da ta'addanci a Afirka, yana da muhimmanci ga ayyukan murkushe ta'addanci da ake yi a fadin duniya. Duk da haka, kamata ya yi kasashe daban-daban su taimakawa kasashen Afirka domin inganta karfin yaki da ta'addanci, bisa tushen mutunta 'yanci da mallakar cikakkun yankunansu, da kuma gudanar da ayyukan soji na hadin-gwiwar kasashe daban-daban, a wani kokari na kawar da barazanar 'yan ta'adda a yankin.
Mista Wu ya kuma jaddada cewar, kasar Sin na son hada kai tare da sauran kasashe, domin tallafawa kasashen dake tsakiya da kuma yammacin Afirka wajen samun ci gaba da zaman lafiya mai dorewa, da bayar da gudummawa ga bunkasar nahiyar Afirka baki daya.(Murtala Zhang)