in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kasance babbar aminiyar Afrika wajen yin hadin gwiwar raya cigaba
2017-04-18 11:05:57 cri

Wani kwararren mai bincike ya bayyana cewa kasashen Afrika suna bukatar kwararru daga kasar Sin, a fannonin cigaban fasaha da harkokin kudade domin hawa matsayi na gaba game da cigaban tattalin ariki da zamantakewa.

Babban daraktan cibiyar nazarin tattalin arzikin Afrika (AERC), Farfesa Lemma Senbet, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a wata ganawa ta baya bayan nan cewa, Sin ta kasance kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya kuma wannan matsayi nata zai iya canza yanayin tattalin arzikin duniya baki daya.

Senbet ya ce, ya yi amana cewar hadin gwiwar Sin da Afrika a fannonin kasuwanci, zuba jari da gina kayayyakin more rayuwa, zai yi matukar samar da sakamako mai kyau wajen samun bunkasuwar nahiyar Afrika.

Masanin wanda dan asalin kasar Habasha ne ya ce yana da kwarin gwiwa cewa duk wani yunkurin kawo cikas game da tattalin arziki da nuna wariya ta fuskar tattalin arziki a Afrika daga yammacin duniya, ba zai iya yin tasiri wajen kawo illa game da huldar dake tsakanin Sin da kasashen Afrika ba.

Senbet ya karyata zargin da ake yiwa kasar Sin cewar tana mu'amala da kasashen Afrika ne don samun albarkatun kasa, inda ya jaddada cewa mu'amalar dake tsakanin Sin da Afrika ta shafi mutunta juna ne da kuma cin moriya ne tsakanin bangarorin biyu.

Kasahen Afrika sun rungumi kasar Sin yayin da suke kokarin fadada hanyoyin tattalin arzikinsu, da tsaron kan iyakoki da karfafa sha'anin siyasa.

Senbet ya yabawa kasar Sin saboda zuba jarinta a kasashen Afrika wajen gina kayayyakin more rayuwa irin na zamani, ya bayyana cewa wannan yunkuri zai kara habaka cigaban tattalin arzikin kasashen Afrika cikin sauri.

Ya kara da cewa kasashen Afrika za su yi matukar cin moriyar shirin nan na raya kasuwanci na ziri daya da hanya daya, wanda mahukunta kasar Sin suka bullo da shi domin kiyaye hanyar dadaddiyar al'adar cinikayya ta kasar Sin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China