in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taro tsakanin kafofin watsa labaru na Afirka da Sin
2017-08-14 20:03:17 cri

An yi wani taron musayar ra'ayi tsakanin kafofin watsa labaru na kasashen Afirka da na kasar Sin a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu a yau Litinin. Masu halartar taron sun hada da mataimakin babban daraktan ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin Guo Weimin, da jakadan kasar Sin dake Afirka ta Kudu Lin Songtian, da wakilan kafofin watsa labarun kasar Sin dake Afirka ta Kudu, da kuma wakilan kafofin watsa labaru 15 na kasashe daban daban dake nahiyar Afirka.

Cikin jawabin da ya gabatar da wajen taron, mista Guo Weimin ya ce, akwai karancin fahimtar juna tsakanin bangarorin Sin da Afirka, idan aka kwatanta da ci gaban da aka samu a fanin hadin gwiwar bangarorin 2. Saboda haka ya ba da shawarar kara yin hadin kai, tsakanin kafofin watsa labaru na bangarorin 2, domin tabbatar da samar da murya mai adalci da sanin ya kamata.

A nasa bangare Timothy Olariwaju, babban editan jaridar' the Sun' ta kasar Najeriya, cewa ya yi har yanzu a Najeriya, mutane da yawa suna sauraron labarai ta hanyar rediyo. Kuma bisa kafa sashen Hausa da gidan rediyon kasar Sin ya yi, ya sa 'yan Najeriya jin dadin sauraron bayanan da ake watsa wa ta harshen Hausa, wadanda suka shafi al'adun kasar Sin, da ayyukan gini da Sinawa suke yi a Najeriya. Mista Olariwaju ya kara da cewa, kokarin da CRI ke yi wajen watsa labarai ga kasashen Afirka yana tare da nasarori, ya kuma yi fatan ganin gidan rediyon ya fara watsa labarai ga karin kasashen dake nahiyar Afirka.

A nasa bangare, babban editan jaridar "the Guardians" ta kasar Tanzania Benjamin Mgana, ya ce, aikin watsa labarai masu alaka da kasashen Afirka, zai taimakawa wajen janyo karin kamfanonin kasar Sin su zuba jari a nahiyar Afirka, da kuma Tanzania, da samar da karin guraben aikin yi, da damammaki a sasssan kasashen. Don haka ya ce yana fatan ganin kafofin watsa labarai na bangarorin Sin da Afirka, sun kara yin hadin gwiwa, bisa samun goyon baya daga gwamnatocinsu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China