An jiyo ministan harkokin cikin gidan kasar Sudan Musa Mohamed Ali Madibo, yana cewa "Dokar kasar ta ba da damar a shirya zanga zangar lumana amma idan an samu amincewar hukumomin kasar, amma kada zanga zangar ta haifa da yin fito na fito, ko tashin hankali, ko kuma rashin zaman lafiya a kasar".
Ministan ya bukaci 'yan kasar da su taimaka wajen dakatar da duk masu yunkurin wargaza zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.
Madibo ya ce, an kafa wasu kwamitoci na musamman tun bayan barkewar zanga zanga a duk fadin kasar, an bayyana cewa kwamitocin da aka kafa sun riga sun fara aikin tantance adadin mutanen da suka hallaka, da kuma irin hasarar da aka tafka na dukiyar gwamnati da bangarori masu zaman kansu.
Tun a ranar 19 ga watan Disamba ne, yankuna da dama a kasar Sudan, ciki har da babban birnin kasar Khartoum, suke cigaba da fuskanta mummunar zanga zanga sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin kasar da tashin farashin kayayyakin masarufi a kasar.
A bisa alkaluman da gwamnati ta fitar, mutane 19 ne aka hallaka a lokacin zanga zangar. (Ahmad Fagam)