Kamfanin dillancin labarai na kasar SUNA ya ruwaito cewa, shugaba AL-Bashir ya yi furucin ne yayin wata ganawar da ya yi da kwamandan hukumar leken asiri da aikin tsaro na kasar, wanda ya kasance karo na farko da ya furta hakan, tun bayan da aka samu barkewar zanga-zanga a kasar don nuna damuwa kan lalacewar tattalin arzikin kasar.
Ban da haka, shugaban ya yi kira ga jama'ar kasar Sudan da kar su saurari jita-jita da magance daukar matakai na takaddama da gwamnati. Ya ce zai dauki takamaiman matakai don kwantar da hankalin jama'a da ba su tabbaci kan tsarin hada-hadar kudi na kasar. (Bello Wang)