Khair al-Zubair, ya ce babban bankin kasar na fatan ba da gudummawa wajen bunkasa alkaluman tattalin arzikin kasar a zahiri, ta yadda alkaluman GDP a fannin za su kai kaso 5.1 bisa dari.
Kaza lika Mr. al-Zubair, ya ce babban bankin zai aiwatar da wasu karin manufofi a bana, da suka hada da dakile hauhawar farashi, da daidai darajar kudaden musaya, da tabbatar da kimar tsarin aikin bankuna a idanun al'ummar kasar, da samar da karin kudaden ajiyar waje, domin wanzar da daidaito a fannin hada hadar kudaden kasar.
Hauhawar farashin kayayyaki a Sudan ya yi mummunan tashi, daga kaso 25.15 bisa dari a watan Disambar 2017, zuwa kaso 68.93 bisa dari a watan Disambar 2018.
Kasar na shan fama da komadar tattalin arziki, tun bayan da Sudan ta kudu ta balle daga cikinta a shekarar 2011, matakin da ya rage mata damar samun haraji daga albarkatun mai da adadinsa ya kai kaso 75 bisa dari. (Saminu Hassan)