A cewar kafar yanar gizo ta Ashorooq, an ayyana wadannan matakai ne bayan kammala zaman kwamitin tsaro na jihar. Ibrahim Mukhtar, shi ne kakakin gwamnatin jihar, ya kuma tabbatar da daukar wannan mataki na gwamnati.
A wani ci gaban kuma, jam'iyyar NCP mai mulkin kasar ta yi tir da barkewar tarzoma a birnin na Atbara. A cewar kakakin jam'iyyar Ibrahim Al-Siddiq, duk wani dan kasa na da ikon bayyana albarkacin bakin sa ta hanyar da ta dace, amma abun da ya wakana a Atbara, sam bai dace da yanayi na wanzar da zaman lafiya da lumana ba.
Ya ce zanga zangar Atbara wani yunkuri ne na wargaza tsaro da zaman lafiya, kuma gwamnati ba za ta lamunci duk wani mataki na gurgunta zaman lafiya ba.
Yayin zanga zangar dai an kona helkwatar jam'iyyar mai mulki dake Atbara, da babban ofishin kananan hukumomi, da wani gidan mai.
Rahotanni sun nuna cewa, da fari an fara zanga zangar ne cikin lumana, kafin daga bisani ta rikide zuwa tashin hankali da ya sabbaba barnata kayayyaki. (Saminu)