in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Rasha sun mika sakon murnar sabuwar shekara ga juna
2018-12-31 16:50:28 cri
A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Rasha Vlładimir Putin suka aike da sakon murnar sabuwar shekara ga juna.

A cikin sakon, Xi Jinping ya bayyana cewa, shekarar bana shekara ce mai matukar muhimmanci a tarihin raya dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha. Kasashen biyu sun cimma manufofin siyasunsu na cikin gida, wanda ya bude sabon babi na raya dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha. Manyan shugabannin kasashen biyu sun yi mu'amala da juna sosai, da kara yin imani da juna a fannin siyasa, da samun kyakkyawan sakamako kan hadin gwiwarsu a dukkan fannoni. Kana bangarorin biyu sun hada gwiwa a harkokin kasa da kasa da yankuna, da taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da adalci da zaman lafiya a duniya.

A nasa bangare, shugaba Putin ya bayyana cewa, a shekarar badi, kasashen biyu za su cika shekaru 70 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu. Ya yi imani cewa, kasashen za su yi amfani da wannan dama wajen kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu kan harkokinsu da harkokin bangarori daban daban. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China