in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi zai halarci bikin cika shekaru 40 na aikewa da sako ga abokai a yankin Taiwan
2018-12-31 15:33:34 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci muhimmin taron cika shekaru 40 na aike sako ga abokan gagwarmaya dake yankin Taiwan, wanda za a shirya gudanarwa a Laraba da safe a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Xi, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, kana shugaban askarawar kasar, zai gabatar da jawabi yayin taron da zai gudana a babban dakin taron jama'a da misali karfe 10 na safiyar ranar Laraba 2 ga watan Janairun sabuwar shekara

Za kuma a watsa bikin kai tsaye ta kafofin rukunin watsa labarai na China Media Group da shafin intanet na kamfanin dillancin labarai na Xinhua (Xinhua.com). Haka kuma za a watsa bikin kai tsaye ta manyan shafukan watsa labarai ciki har da people.com.cn da cctv.com da china.com.cn da kuma manhajan watsa labarai na jaridar people's Daily, da kamfanin dillancin labarai na Xinhua da babban gidan talabijin na kasar Sin, CCTV. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China