in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya aika da sakon jaje ga takwaransa na Indonesia
2018-12-24 19:08:55 cri
A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sako ga takwaransa na kasar Indonesia, don jajanta masa dangane da aukuwar babbar igiyar ruwan teku mai karfin gaske ta tsunami, a mashigin tekun Sund a karshen makon da ya gabata.

Shugaba Xi ya ce, ya yi bakin ciki da jin labarin aukuwar wannan bala'in nan na tsunami, wanda ya yi sanadiyyar hasarorin rayuka da kadarori, kuma a madadin gwamnatin kasar Sin da al'ummarta da kuma shi kansa, yana mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.

Shugaban ya kuma yi fatan al'ummar kasar Indonesia za su gaggauta farfado da kasarsu, a karkashin gwamnatin kasar mai ci.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China