in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya buga waya ga shugaban kasar Amurka Trump
2018-12-30 16:45:00 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya buga waya ga shugaban kasar Amurka Donald Trump a ranar 29 ga wannan wata bisa gayyatar da aka yi masa.

Trump ya bayyana cewa, raya dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin yana da muhimmanci sosai, wanda ya yi matukar jawo hankalin dukkan duniya. Ya ce yana farin ciki matuka game da aikin da tawagogin kasashen biyu suke yi na kokarin tabbatar da matsaya guda da ya cimma da shugaba Xi Jinping a yayin ganawarsu a kasar Argentina. Ana samun ci gaba kan shawarwarin game da wannan batu, kuma yana fatan za a cimma sakamako mai amfanawa jama'ar kasashen biyu har ma ga jama'ar kasashen duniya gaba daya.

Xi Jinping ya jaddada cewa, shekarar badi shekara ce ta cika shekaru 40 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Amurka. Sin tana dora muhimmanci sosai kan raya dangantakar dake tsakaninta da Amurka, da nuna yabo ga kasar Amurka domin tana son raya hadin gwiwa da dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. Sin tana son yin kokari tare da kasar Amurka wajen takaita fasahohin raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka da aka samu a shekaru 40 da suka gabata, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da sojoji, da dokoki, da yaki da miyagun kwayoyi, da kananan gwamnatocin kasashen biyu, da al'adu da sauransu, da kiyaye yin mu'amala kan manyan batutuwan kasa da kasa da yankuna, da girmama moriyar juna, da sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakaninsu bisa tushen yin hadin gwiwa, da kiyaye zaman lafiya, don kara amfanawa jama'ar kasashen biyu har ma ga jama'ar dukkan kasashen duniya baki daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China