in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana gudanar da zaben shugaban kasa a DRC
2018-12-30 20:26:59 cri

Masu jefa kuri'a a jamhuriyar demokradiyyar Kongo sun fara jefa kuri'unsu a yau Lahadi, a muhimmin zaben da ake sa ran zai samar da makoma ga kasar ta tsakiyar Afrika.

Zaben, wanda a baya ya fuskanci matsaloli na yawan dage ranakun gudanar da shi, ana fatan za'a zabi mutumin da zai gaji shugaban kasar mai ci Joseph Kabila, wanda ke kan ragamar mulkin kasar tun a shekarar 2001, kana ana fatan za'a samu nasarar sauya shugabancin kasar cikin kwanciyar hankali da lumana.

Tun da misalin karfe 6 na safiyar yau Lahadi, agogon babban birnin kasar Kinshasa, wato karfe 5 ke nan agogon GMT, aka bude rumfunan zaben kasar. Masu kada kuri'a sun fito, duk kuwa da ruwan saman da ake shekawa kamar da bakin kwarya da aka fara tun sa'o'i biyu da suka gabata.

Shugaban kasar Joseph Kabila da sauran 'yan takarar neman shugabancin kasar na daga cikin wadanda suka fara jefa kuri'unsu a unguwar Gombe dake Kinshasa. Bayan da ya kada kuri'arsa, Kabila ya ce, duk da ruwan saman da ake shekawa, "Mutanenmu a shirye suke su kawo karshen kalubalolin dake tattare da wannan zabe, baki dayanmu muna rubuta wani labarin ne da ya shafemu."

Dan takarar babbar jam'iyyar hadaka wanda ke da aniyar maye gurbin Kabila, Emmanuel Ramazani Shadary, ya fada bayan kada kuri'arsa cewa, yana da kwarin gwiwar samun nasarar lashe zaben.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China