in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta bukaci a ba da damar kai dauki a DRC game da barkewar cutar Ebola
2018-08-13 09:52:58 cri

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) a ranar Lahadi ta bukaci a ba da damar kai dauki don dakile yaduwar annobar cutar Ebola wadda ta bulla kwanan nan a jamhuriyar deomkaradiyyar Kongo (DRC), wannan shi ne karon farko da cutar ta barke a wani yanki mafi cunkoson jama'a mai fama da rikici.

Kasa da mako guda tun bayan ayyana sabon rahoton bullar cutar ta Ebola a DRC, darakta janar na hukumar WHO Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, da daraktan WHO mai kula da shiyyar Afrika Dr. Matshidiso Moeti, da mataimakin darakta janar na hukumar WHO mai kula da kai daukin gaggawa Dr. Peter Salama, sun kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu zuwa birnin Beni da cibiyar lafiya ta Mangina dake arewacin lardin Kivu, a DRC. Mangina, mai tazarar kilomita 30 daga birnin Beni, ta kasance a matsayin wata cibiyar kula da barkewar cututtuka kuma a can ne aka gudanar da gwaje gwaje mafi yawa na tabbatar da bullar cutar a halin yanzu.

"WHO tana kira da a ba da damar shiga yankunan cikin sauki ga dukkan masu kai dauki don agazawa mutanen da cutar ta kama," Dr. Tedros ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci yankin. "Dukkan illahirin masu kai dauki zuwa yankunan, kamata ya yi a ba su damar shiga yankunan da ake fama da rikici kai tsaye domin su gudanar da ayyukansu da nufin shawo kan bazuwar cutar. Dole ne kuma a samar da magunguna ga mutanen da suka kamu da cutar, da kuma yin riga kafin yaduwar cutar."(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China