in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO: Akwai abun damuwa game da sake barkewar cutar Ebola a DRC
2018-08-16 09:35:12 cri

Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya nuna matukar damuwa game da yanayin da ake ciki a janhuriyar dimokaradiyyar Congo, sakamakon sake bullar cutar Ebola mai saurin kisa a yankin da ke da yawan jama'a, baya ga tashe tashen hankula da ke kara ta'azzara yanayin.

Mr. Tedros ya bayyana irin mummunan yanayin da ake ciki a lardin arewacin Kivu ne, a yayin wani taron karawa juna sani, bayan ziyarar da ya kai kasar ta Congo, yana mai cewa, tashe tashen hankula na samar da hanya mai sauki ta yaduwar cutar.

A cewar sa, daga watan Janairun farkon wannan shekara zuwa yanzu, akwai sama da kungiyoyin 'yan tawaye sama da 100 dake cin karen su babu babbaka a lardin, an kuma samu aukuwar hare hare sama da 120 a tsakanin farkon shekarar zuwa yanzu.

Babban daraktan na WHO ya ce, ko a lokacin da yake ziyarar aiki a kasar, an kai hari garin Beni mai nisan kilomita 15 daga inda ya yada zango, wanda kuma daya ne daga manyan biranen dake arewacin Kivu.

Don haka ya ja hankalin masu ruwa da tsaki a kasar da su kai zuciya nesa, su kauracewa daukar matakan da ka iya kara rura wutar rikici, duba da cewa cutar Ebola ba za ta bar wani bangare na al'ummar kasar ba. Ya ce, kasancewar yankin da fadace tadace ke kara yaduwa, zai baiwa cutar Ebola damar yaduwa ba tare da wani tarnaki ba.

Akwai dai dubban jama'a mazauna lardin arewacin Kivu, kuma zirga zirga tsakanin su, da kuma cudanya tsakanin masu gujewa gidajen su a yanki wadanda yawan su ya haura miliyan guda, na haifar da babban kalubale ga yunkurin da WHO da abokan huldar ta ke yi, na kai dauki ga yankin, a cewar Mr. Tedros.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China