in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF na kara tallafawa makarantun yankunan da annobar Ebola ta shafa a DRC
2018-08-29 10:27:52 cri

Asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF) ya sanar a jiya Talata cewa, yana daukar matakan da suka dace domin samun nasarar ganin an bude makarantu don fara karatu na wannan shekarar a yankunan da cutar Ebola ta shafa a gabashin jamhuriyar demokaradiyyar Kongo (DRC).

UNICEF ya ce, akwai makarantu kimanin 250 dake yankuna da Ebolar ta shafa, wadanda ke kunshe da dalibai kimanin 82,500.

Sabbin matakan da za'a dauka sun hada da horas da shugabannin makarantu da malaman makaranta sama da 1,750 game da yadda cutar Ebola take da kuma matakan da suka dace a dauka wajen samun kariya daga kamuwa da kwayar cutar, da daukar matakan gano cutar cikin gaggawa, da kebe yaran da ake ganin suna nuna alamomin kamuwa da cutar Ebolan, da kuma kai yaran asibiti, da rarraba kananan na'urorin gwada yanayin jiki, da kafa cibiyoyin wanke hannaye da kuma rarraba hotunan dake fadakarwa don rigakafin cutar a dukkan makarantu.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce, nan da kwanaki 7 zuwa 10 masu zuwa su ne mafiya muhimmanci wajen yaki da yaduwar kwayoyin cutar Ebola a gabashin Kongo. Rahotannin baya bayan nan sun nuna cewa, an samu rahoton bullar cutar Ebolan kimanin 111, da wasu 83 da aka tabbatar sun riga sun kamu da cutar, da wasu 28 da ba'a tabbatar ba, kana akwai wasu mutane 75 da ake zaton cutar ta yi sanadiyyar kashe su.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China